Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wata tirela makare da giyar da ake kokarin shiga da ita jihar.

An kama motar ne dauke da kiras 1,500, wato kimanin kwalba 18,000 a ranar Lahadi a kan hanyar Gwarzo zuwa Kano.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sashen yada labaranta ya fitar ranar Litinin, dauke da sa hannun Babban Kwamandanta, Harun Muhammad Ibn Sina.

Sanarwar ta ambato Babban Kwamandan na cewa, motar da aka kama gaba dayanta giya ce.

Kuma irinta suna da kusan tirela 10. ba don aikin da Hisbah ta yi na kama ta ba, da duk a Kano za a shanye ta.
Ibn Sina ya ce ya kamata jama’a su san cewa har yanzu sayarwa, rabawa, dakon giya haramun ne a jihar Kano, kuma duk inda suka gan ta za su kama, nan da lokaci kadan za su yi bikin farfasata.