Connect with us

Labaran jiha

Kungiyar SERAP Ta Zargi Gwamnatin Tarayya Kan Kin Bincikar Wasu Kudade

Published

on

An zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gazawa wajen binciken kudaden da aka wawure a dukkan matakan gwamnati.

Wata kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam da sanya idanu kan harkar tafiyar da kudaden al’umma (SERAP) wacce ta yi wannan zargin, ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kotu.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce matakin shigar da karar ya biyo bayan gazawar da gwamnatin tarayya tayi wajen binciken makudan kudaden da aka ce an kashe sama da tiriliyan wajen kula da muhalli a dukkan matakan gwamnati, tun daga tarayya da jihohi da kananan hukumomi daga shekarar 2001 zuwa yau da kuma tabbatar da hukunta wadanda ake zargi da aikata almundahana da dukiyar mutane.

A cewarsa, a kwanan baya asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce akalla mutane 600 ne suka mutu yayin da miliyan 1.3 suka rasa matsuguni sakamakon ambaliyar ruwa da ta addabi mafi yawan jihohin kasar, tare da lalata kadarori na biliyoyin kudi.

A cikin karar da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman kotun da ta umarci shugaba Buhari da ya gaggauta bincike kan yadda gwamnatoci suka kashe wadannan makudan kudaden kula da muhallin tun daga Matakin tarayya, jiha da kananan hukumomi daga shekarar 2001 zuwa yau.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Soke Komawa Makaranta Ranar Litinin

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta soke komawar ɗalibai makaranta ranar Litinin.

 

Hakan na kunshe a wani sakon murya da kwamishinan ilimi a jihar Umar Haruna Doguwa ya sanar.

 

Ya ce an dakatar da komawa makarantar ne saboda wasu abubuwa dasu ka taso.

 

Sannan ya ce za a sanar da ranar komawa nan gaba kaɗan.

 

Kwamishinan ya bai wa iyaye hakuri dangane da jinkirin da aka samu.

Continue Reading

Labaran jiha

Ambaliyar Ruwa – Mutane 20 Sun Mutu A Yobe

Published

on

Mutane 20 ake fargabar sun mutu yayin da mutane 3,000 su ka rasa muhallinsu a jihar Yobe.

 

Shugaban ƙaramar hukumar Bade Babagana Ibrahim ne ya bayyana haka ya ce lamarin ya faru sakamakon ruwan kamar da bakin ƙwarya.

 

Ya ce gwamnatin na ƙoƙarin samar da kayayyakin agaj kamar abinci, magunguna, da taftataccen ruwan sha don kare su daga kamuwa daga cutuka.

 

Sai dai ya ce akwai buƙatar agajin gwamnatin tarayya duba ga yawan masu gudun hijirar.

 

Shugaban ya ce makonni biyu kenan aka shafe ana samun ruwan sama wanda ya yi sanadiyyar ambaliya.

 

Lamarin ya shafi Gashua tare da umartar mutanen da ke rayuwa a wuraren da ambaliyar na iya shafa da su kauce tare da barin gidajensu.

Continue Reading

Labaran jiha

Bayan Ɓarkewar Zanga-zangar Kan Tsadar Man Fetur Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Umarnin Fito Da Manyan Motoci Da Ɗaukar Mutane Kyauta

Published

on

Gwamnan jihar Kwara Abdurrahman Abdurrazak ya bayar da umarnin fitar da motoci a kwaryar birnin jihar don saukaka harkar sufuri.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan da jama’a ke kokawa danane da tashin farashin man fetur a ƙasar.

Babban sakataren yaɗa labaransa Rafiu Ajakaye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce za a ɗauki mutane zuwa manyan wurare kyauta

Wannan dai na zuwa ne yayin da masu ababen hawa su ka tafi yajin aiki sanadin ƙarin farashin mai wanda hakan y sa fasinjoji su ka yi cirko cirko a tituna.

Gwamnan ya bai wa jama’ar jihar hakuri dangane da halin da ake ciki na tsadar man fetur.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: