A cikin wata sanarwa da Kwamitin yakin neman zaben Tinubu ta fitar ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai wa jabtawa dan takararta halartan muhawarar da wata kungiya ta shirya ba.

A wata sanarwa da Arise TV ta fitar kwanan nan ta bukaci dukkan ‘yan takarar da su mutunta kundin tsarin mulkin kasar kuma su halarci muhawarar da ta shirya.

A baya dai Tinubu ya ki amsa gayyatar tun farko, har ma ya sha alwashin ba zai halarci wasu muhawarar ba.

Tinubu ya ki amsa gayyatar Muhawarar a karon farko wanda aka shirya kan tsaro da tattalin arziki a ranar 6 ga watan Nuwamba. Ya ce muhawarar ta ci karo da jadawalin yakin neman zabensa.

An maye gurbinsa da Kola Abiola, dan takarar jam’iyyar Peoples Redemption Party.

sai kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu wakilcin abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

APC ta zargi gidan talabijin din da nuna son kai ga Tinubu kuma ta sha alwashin ba za ta halarci duk wata muhawara da Arise TV ta shirya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: