Majalisar dattawan Najeriya ta ce ta gano yadda aka cusa naira biliyan 206 da aka sanya a boye a cikin kasafin kudin ma’aikatar Walwala da Jinkai.

Majalisar ta ce an sanya kudin ne da gangan, domin sayen makamai da kayan aikin sojoji.

Wannan ya fito ne lokacin da Majalisar Dattawa ta gano cewa kasafin kudin ma’aikatar ya samu wani bakon kudi har Naira biliyan 206 da aka kara ba tare da cikakken bayani ba.

Sadiya Umar Farouq, ta bayyana mamakin gano abin da majalisar dattawa ta yi, lokacin da aka nemi ta yi bayanin kasancewar makudan kudade a cikin kasafin kudin ma’aikatar ta.

Sadiya ta ce A wani rahoto da manema labarai su ka rawaito ministan tace itama tayi mamaki yadda taga kudi kusan naira biliyan 206 a ciki kuma akai ikirarin na siyan makamai ne da kayan sojoji, kuma a ma’aikatar jinkai.

Shi ma babban sakataren ma’aikatar Sani Gwarzo ya bayyana yadda aka samu naira biliyan 206 a cikin kasafin su a matsayin wani kuskure da ya kamata a binciki ma’aikatar kudi kan kan wannan batu.

Ya ce yana da kyau gwamnati tayi tsari mai kyau na yakar cin hanci da rashawa a tsakanin hukumomin gwamnati da kuma bin diddigin yadda suke kashe kudaden su wanda suka sanya a kasafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: