Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan gidaje da raya birane na jihar Benue, Ekpe Ogbu.

Channels TV ta rawaito cewa an sace Ogbu a mararrabar Adankari da ke hanyar Otukpo-Ado a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.
Manema labarai sun rahoto cewa kwamsihinan ya halarci wani taron coci, inda Sanata Abba Moro, mai wakiltan Benue ta kudu ya mika lamuran kamfen dinsa da ya kaddamar ga Allah, a hanyarsa ta zuwa kauyensa da ke NDEKMA abun ya faru.

Mai ba gwamnan jihar, Samuel Ortom shawara kan harkokin tsaro Kanal Paul Hemba (mai ritaya) ya tabbatar da sace Ogbu.

Hemba wanda ya zanta da manema labarai kan sace kwamishinan ya bayyana cewa rundunar yan sanda a Otukpo ta yi nasarar samo motar Hilux da Ogbu ke tafiya a ciki.
An kuma tattaro cewa maharan basu kira kowa daga dangin kwamishinan ba, amma dai an fara kokarin ganin an kubutar da shi daga hannun miyagun.
A baya, an yi garkuwa da wani limamin katolika, farfesan jami’ar jihar Benue da wani dan siyasa daga Otobi a wannan wajen a lokuta mabanbanta.