Tsohon sakataren yada labarai na jamiyyar PDP kuma mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP Atiku Abubakar, Kola Ologbondiyan, ya ce dan takararsu nan a PDP zai ziyarci dakin taro na Chatham kadai idan an gayyace shi.

Ologbondiyan ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Arise TV a safiyar yau Laraba cikin wata muhimmiyar tattaunawa dake da jibi da karatowar babban zaben shekarar 2023 a Najeriya.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya kasance bako a dakin taro na Chatham dake kasar Ingila, inda ya bayyana wasu daga cikin manufofinsa da kudurorinsa a manyan bangarori daban daban kamar tsaro, tattalin arziki, ilimi da kuma fasaha wanda zai tabbatar da su aikace da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2023.

Hakan na zuwa ne a rana guda yayin da Atiku Abubakar ke gudanar da yakin neman zabe a jihar Lagos, wanda ya tabattarwa da al’ummar jihar Lagos kudirinsa na sauya fasali da zamanantar da matatun mai don habaka harkar sarrafa danyen mai a cikin gida Najeriya.

A kan batun ziyarar da Bola Tinubu ya yi zuwa dakin taro na Chatham, Ologbondiyan ya ce Atiku Abubakar zai ziyarci gurin kadai idan ya samu katin gayyata, inda ya kara da cewa yana da yakinin da tambayoyin da za a yi a gurin dan takararsu na PDP zai amsa su cikin sauki da nuna kwarewa, ba kamar yadda abin ya kasance ba ga dan takarar jam’iyar APC.