Gwamanatin kasar Burtaniya ta ce babu wani dan takarar shugaban kasa da take goyon baya a zaben Najeriya na shekarar 2023.

Jakadiyar Burtaniya a Najeriya Catriona Laing ta sanar da hakan bayan wata ganawar sirri da kwamitin gdanarwa na jam’iyyar APC na kasa a birnin Abuja.

Jakadiyar ta Burtaniyan ta kara da cewa babu wani dan takara da Burtaniya ta fi so, kasar tafi damuwa daga anyi sahihin zabe mai cike da kwanciyar hankali, ta cigaba da cewa zatai aiki da dukkan ‘yan takarkarun shugabancin Najeriya daga dukkan jam’iyyu.

Sannan ta kuma jaddada amincewar gwamnatin Burtaniya da kudurin Najeriya na tabbatar da dorewar dimukuradiyya da yadda shugaba Buhari ya lashi takobin gudanar da zabuka masu inganci da kwanciyar hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: