Majalisar dattawa ta sanya ranar 13 ga watan Disamba domin nazari kan sabuwar dokar babban bankin Najeriya CBN ta kayyade kudaden da jama’a zasu iya cirewa a rana.

Majalisar dai ta nuna damuwa a zamanta na ranar laraba kan sabon tsarin na CBN.
A karkashin sabon tsarin, mafi yawan kudin da daidaikun mutane zasu iya cirewa a mako ta hanyar POS shine naira 100,000 yayin da kamfanoni zai iya cire naira 500,000.

Sabon tsarin ya kuma kayyade naira 20,000 a matsayin iya abinda mutum zai iya cirewa a kwacce rana.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar Sanata Phillip Aduda, ya ja hankalin majalisar kan yin taka tsan-tsan game da sabon tsarin, domin a cewarsa tsarin zai shafi ‘yan kasa musamman kananan ‘yan kasuwa.
Da yake mayar da martani kan lamarin shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya gargadi CBN kan sabon tsarin inda ya umarci kwamitin harkokin bankuna na majalisar da yayi aiki tare da CBN domin tattaunawa kan lamarin.