Matar dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC Sanata Oluremi Tinubu ta ce tikitin musulmi da musulmi ya bude wani sabon salo kuma sabon babi a siyasar kasar nan a shekarar 2023.

Da take buga misali da tikitin shuggaban kasa na musulmi biyu a jam’iyyar APC da yadda hakan ya jawo cece-kuce, mai dakin ta Tinubu ta yi fatan cewa nan gaba kuma a sami tikitin kirista da kirista a kasar.

Oluremi ta yi wannan batu ne a yayin gangamin yakin neman zabe na jam’iyyar APC na mata ta shiyyar kudu maso yamma wadda ya gudana a jihar Legas.

Kana ta mika godiyar ta ga uwar gidan shugaba Muhammadu Buhari, aisha Buhari, wadda aka turawa katin gayyata amma bata sami halartar taron ba.

Sanata Uluremi dai ita ce mace ta farko da ta zama sanata har sau uku, inda ta ce wannan babbar dama ce a gareta, tun a shekarar 2007 da mijinta yabar gwamna ta cigaba da aikin ga al’ummmarta a cewarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: