Connect with us

Labaran jiha

A Gaggauta Yakar Ta’addanci A Yankin Yammacin Afrika – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a gaggauta kaddamar da mataki kan yaki da ta’addanci a yankin yammacin Afirka.

Shugaban kasar Najeriya ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wurin taron shugabannin ECOWAS karo na 62 wanda ya gudana a Abuja. Ya kara da cewa akwai bukatar sauya salon yaki da ‘yan ta’adda a yankin yammacin Afirka.

A cewarsa, wannan yunkuri zai karfafa kokarin gwamnatocin yanki wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a yammacin Afirka. Ya yi kira ga sabon tawagar ECOWAS wanda Dakta Omar Alieu Toure yake jagoranta kan gaggauta kammala nazari na sake fasalin kungiyar domin samun inganta yankin yammacin Afirka.

Buhari yace dole ne kungiyar ECOWAS ta gudanar da aiki ba dare ba rana wajen ganin an kammala yin nazari kan sauya fasalin ka’idojin shugabanci da na dimokuradiyya a yankin yammacin Afirka, domin karfafa kokarinsu wajen gudanar da shugabanci mai inganci ga kasashensu.

Da yake yi wa shugabannin yankin maraba, Buhari ya ce taron wannan shekarar shi ne na 8 da Nijeriya ke shiryawa, dukkan wadannan taruka ciki har da na wannan shekara Nijeriya ce ke shiryawa wanda hakan ke kara karfafa dangantakarsu domin bullo da hanyoyin magance matsalolin kasashensu da kuma al’ummominsu, a cewar shugaba Buhari.

Shugaban Buhari ya jinjina wa takwaransa na kasar Ghana, Kuffour Addo-Nana wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar bisa shugabancinsa da taya murna ga Shugaban Guinea Bissau, Umaro Embalo kan tabbatar da daukar ragamar shugabancin kungiyar.

Buhari ya gode wa shugabannin bisa goyon bayansu wajen rawar da suka taka lokacin cutar Korona kan hadin kai yankunan yammacin Afirka.

Tun da farko dai a harabar sabon shalkwatan ECOWAS, Buhari ya nuna godiyarsa ga gwamnatin China bisa tallafin kudade da kayan aiki wajen gina shalkwatan kungiyar.

Gini da aka sanya wa suna idon yammacin Afirka ana tsammanin za a kammala shi ne nan da watanni 26, yana da manyan cibiyoyi guda uku wadanda suka hada da na shalkwatan kungiyar ECOWAS da kotun kungiyar da majalisarta.

A cewar shugaban kasan, dama suna jiran wannan rana tun 10 ga watan Yulin 2019 lokacin da ECOWAS da mutanen China suka rattaba hannu kan kaddamar da kyautar difolomasiyya ga kasashen yammacin Afirka.

A nasa jawabin, Jakadar kasar China a Nijeriya, Cui Jianchun ya ce, Tallafin gina sabon shalkwantan ECOWAS yana zuwa ne sakamakon kawance da kasar China take da shi da kasashen yammacin Afirka.

Jianchun yace za su ci gaba da bunkasa kawance tsakanin China da Afirka, sannan a shirye suke domin bayar da tallafi wajen ci gaban Afirka zuwa mataki na gaba.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Babu Batun Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Abba – Gwamnatin Kano

Published

on

Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.

Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.

Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.

Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.

Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.

Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.

Continue Reading

Labaran jiha

Gwamnatin Kwara Za Ta Bai’wa Ma’aikatan Jihar Tallafi

Published

on

Gwamnan Jihar Kwara Abdurrahman Abdulrazak ya amincewa da bai’wa ma’aikatan Jihar, Alawus-alawus da ake bai’wa ma’aikata kowanne wata.

Kwamishiniyar kudi ta Jihar Hauwa Nuru ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X na gwamnatin Jihar a yau Litinin.

Kwamishinar ta ce daga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin a Jihar, ciki harda ma’aikatan Kananan hukumomin Jihar.

Nuru ta ce shirin bai’wa ma’aikata tallafin kudin zai gudana na ne tsawon watanni uku daga watan Oktoba da ya gabata zuwa Disamba mai kamawa.

Nuru ta bayyana cewa bayar da tallafin zai taimaka matuka wajen rage tasirin sauyin da aka samu a harajin PAYE, wanda ake cirewa bayan samar da sabon mafi karancin albashin ma’aikatan.

Acewar Hauwa tallafin na a matsayin abin da ya dace domin tallafawa ma’aikatan, a lokacin da suke kokarin sabawa da sabon tsarin PAYE da aka samar bisa dokar harajin shiga na sirri.

A karshe Kwamishinar ta bukaci ma’aikatan Jihar da su tabbatar da ganin sun yi rajista da hukumar rajista ta jihar KWSRRA, inda ta bayyana cewa dukkan wanda bashi da rajistar ba zai samu alawus din ba.

Continue Reading

Labaran jiha

An Samu Karin Farashin Man Fetur A Legas

Published

on

Rahotanni na nuni da cewar an sake samun karin farashin man fetur a jihar Legas jiya Talata

Mutane a jihar Legas sun wayi gari da ganin sabon farashin man fetur.

An siyar da man kan naira 1,025 kowacce lita maimakon naira 998 da ake siyarwa a karin da aka yi baya bayan nan.

Gidajen mai na NNPC ke siyar da mai naira 1,025 a Legas.

A babban birnin tarayya Abuja ma an siyar da lita guda naira 1,060 kowacce lita

Wannan na zuwa ne yayin da farashin gangar mai ta fadi a kasuwar duniya.

A baya kamfanin mai na NNPCL ya ce ya samu karin farashin mai da yake siyowa daga matatar mai ta Dangote.

Dalili kenan da ya sa shi ma ya ƙara farashinsa a gidajen man sa.

A cewar kamfanin, a halin yanzu kasuwa ce ke halinta, sai dai kuma farashin gangar mai sauka ya yi a wannan lokaci.

Idan za q iya tunawa a baya, mun baku labarin yadda mutane da dama su ka ajiye ababen hawansu sakamakon tsadar man fetur da ake fuskanta a Najeriya.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: