Wata babbar kotu da ke Jihar Ekiti ta yankewa wani matashi mai shekaru 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kamashi da aka yi da laifin yiwa wata matashi mai shekaru 20 makobciyar sa fyade.

Kotun ta bayyana cewa tana tuhumar matashin da laifuka guda bakwai ciki harda mallakar bindigu guda biyu da kuma zama dan kungiyar asiri da aikata fyade.

A wata takarda tuhuma da aka gabatar wa da kotun ana kuma zargin matashin da abokin sa da ya tsere da yin fashi a wani shago inda su ka kwashe kayan shagon da kudinsu ya kai sama da naira miliyan 1.8.

Wadda matashi yayiwa fyaden ta bayyana cewa yayi mata barazana ne da bindigan har ta kai ga yayi mata fyaden.

A yayin shari’ar lauya mai gabatar da kara ya gabatar wa da kotun shaidu biyar yayi da lauyan wanda ake gabatar da kara bai gabatar da shaida ko daya ba.

Bayan kammala gabatar wa da kotun shaidun Alkalin kotun ya yanke wa wanda ake zargin hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: