Akalla mutane uku ne su ka rasa rayukan su a yayin wani hari da ‘yan bindiga su ka kai kauyukan Amtawalam da Pobaure da ke karamar hukumar Billire a Jihar Gombe.

Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Adamu Kupto Dishi ne ya bayyana hakan.
Dishi ya ce ‘yan bindigan sun kai harin ne a tsakar daren ranar Juma’a.

Kupto ya kara da cewa bayan sanar da shi faruwal lamarin ya kira jami’an sajo da maharba domin isa gurin.

Kwamishinan ya ce bayan farwal lamarin da safe gwamnan Jihar ya turasu gurin da lamarin ya faru.
Kazalika ya ce gwaman Jihar ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar SEMA ta bai wa wadanda lamarin ya shafa tallafi domin rage musu radadin a sarar dasu ka yi.
Anashi bangaren kwamishinan yan sandan Jihar ya bayyana cewa shima ya ziyarci yankin da abin ya faru.
Kwamishinan ya ce dukiya mai yawa ta salwanta a yayin harin.