Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi Allah wa-dai da sace jajirai biyar sabbin haihuwa a wani Asibiti da wasu batagari su ka yi a Jihar Anambra.

Mataimakin shugaban kan harkikin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan na cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Bayan faruwar lamarin shugaban ya bayar da umarnin sanya matakan tsaro a cikin Asibitin domin kaucewa sake faruwar hakan.

Shugaban ya bayar da umarnin kawo karshen aikata laifuka a yankunan nan bada dadewa ba.

Shugaban ya kuma ce dole ne a gaggauta kawo karshen hakan domin kawo karshen batagarin.