Hukumar shirya jarrabawar ta yammacin Afrika WAEC ta rufe wasu cibiyoyi da ake gudanar da jarrabar a makarantu 61 na Jihar Kogi.

Hukumar ta dauki wannan hukuncin ne sakamakon kama cibobiyoyin da aka yi da magudin jarrabawar.

Kwamishinan Ilmi kimiyya da fasaha na Jihar Wemi jones ne ya bayyana hakan a gurin kammala rabon takardu jarrabawar wasu darussa a makarantun sakandire 95 da ke mazabar Kogi ta yamma a ranar Juma’a.

Acewarsa Ma’aikatar sa za ta dauki tsatstsaran mataki akan dukkanin principal din kowacce makaranta da su ka kawowa Jihar Nakasu tare da kunya tata.

Kwamishinan ya ce za su kafa kwamitin da zai yi aikin gano laifukan dukkan wani Principal domin yi masa hukunci.

Wemi ya ce hakan ba zai yuwu ba gwamnati ta ringa kashe kudade a fanni ilmi amma wasu mutane su dinga cin diddigen ta wanda hakan ne ya ke batawa Jihar suna.

Kazalika kwamishinan ya ce tun a shekarar 2019 da ta gabata ne hukumar ta WAEC ta rufe cibiyoyi 51 na yin jarrabawar a Jihar.

Kwamishinan ya ce tun bayan rufe cibiyoyin ma’aikatar ta dauki mataki akan wanda hakan ya sanya wasu makarantun su ka daina.

Wemi ya bayyana cewa sai a shekarar 2020 zuwa 2021 aka samu makaranta daya da aikata laifin.

Kwamishinan ya ce a shekarar 2022 da mu ke ciki abin ya haura daga na 51 na shekarar 2019 zuwa makarantu 61.

Ya kara da cewa a ranar Alhamis hukumar ta sake aikewa ma’aikatar ilmin takarda na sake rufe wasu cibiyoyin jarrbawar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: