Wasu matasa a Jihar Nasarawa sun cirewa wani jigo a jam’iyyar APC reshen Jihar kaya tare da yi masa duka a lokacin da jam’iyyar ta ke gudanar da yakin neman zaben ta.

Shugaban kwamitin shawara na jam’iyyun IPAC a Jihar shine ya tabbatar da faruwal lamarin.

Ya ce matassa sun aika-aikar ne a fadar Sarkin Lafia a ranar Alhamis.

Shugaban ya kara da cewa ana kyautata zaton matasan magoya bayan jam’iyyar ne su ka aikata hakan a cikin mutane.

Bayan faruwal lamarin Shugaban jam’iyyun Ogah Doma ya yi kira ga matasan Jihar da su nesanta kansu da aikata ta’addanci a fadin Jihar.

Doma ya ce abind matasan su ka aikata sun yi shine akan rashin tunani,inda ya ce su guji biyewa wasu ‘yan siyasa da su ke amfani da su wajen ciwa abokin takarar su zarafi.

Shugaban ya kara da cewa abinda matasan su ka abin allah wadai ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: