Connect with us

Labaran jiha

Hukumar Zabe Ta Kasa INEC Ta Bude Fara Bayar Da Katunan Zabe

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa tuni ta fara bayar da katinan zabe Wanda su ka yi rijista katin zaben a yau Litinin 12 ga watan Disambar 2022.

Jami’ar hukumar ta INEC Zainab Aminu ita ce ta sanar da jaridar BBC yadda za a bayar da katinan wanda tu ni aka fara bayarwa a yau.

Ta ce wadanda za a baiwa katinan zaben su ne wadanda su ka bayar da bayanan su daga farkon fara yin rijistar a watan yuli zuwa Disamba2021.

Sannan akwai wadanda katinan su ya bata suma za a ba su na su katin ko ya lalace harta kai na’ura ba ta iya ganewa.

Sannan ko wadanda su ke bukatar a sauya musu mazaba ko canjin gari suma za su karbi katinan su bayan sun zo da dukkan shaidar da aka ba su ta amsar kati zabe.

An fara rabon katin yau Litinin 12 ga watan Disamba sannan za a rufe 23 ga watan junairu 2023.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Gwamnan Legas Ya Yiwa Fursunoni Afuwa

Published

on

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayar da umarni sakin fursunoni 55 daga gidajen gyaran hali daban-daban na fadin jihar.

Kwamishinam shari’a na jihar, Lawal Pedro, SAN, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu.

Gwamna ya amince da sakin mazauna gidan gyaran halin ne bisa shawarwarin da majalisar duba yiwuwar yiwa fursunoni afuwa ta jihar.

Continue Reading

Labaran jiha

Babu Batun Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Abba – Gwamnatin Kano

Published

on

Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.

Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.

Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.

Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.

Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.

Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.

Continue Reading

Labaran jiha

Gwamnatin Kwara Za Ta Bai’wa Ma’aikatan Jihar Tallafi

Published

on

Gwamnan Jihar Kwara Abdurrahman Abdulrazak ya amincewa da bai’wa ma’aikatan Jihar, Alawus-alawus da ake bai’wa ma’aikata kowanne wata.

Kwamishiniyar kudi ta Jihar Hauwa Nuru ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X na gwamnatin Jihar a yau Litinin.

Kwamishinar ta ce daga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin a Jihar, ciki harda ma’aikatan Kananan hukumomin Jihar.

Nuru ta ce shirin bai’wa ma’aikata tallafin kudin zai gudana na ne tsawon watanni uku daga watan Oktoba da ya gabata zuwa Disamba mai kamawa.

Nuru ta bayyana cewa bayar da tallafin zai taimaka matuka wajen rage tasirin sauyin da aka samu a harajin PAYE, wanda ake cirewa bayan samar da sabon mafi karancin albashin ma’aikatan.

Acewar Hauwa tallafin na a matsayin abin da ya dace domin tallafawa ma’aikatan, a lokacin da suke kokarin sabawa da sabon tsarin PAYE da aka samar bisa dokar harajin shiga na sirri.

A karshe Kwamishinar ta bukaci ma’aikatan Jihar da su tabbatar da ganin sun yi rajista da hukumar rajista ta jihar KWSRRA, inda ta bayyana cewa dukkan wanda bashi da rajistar ba zai samu alawus din ba.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: