Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya kaddamar da yakin neman zabensa na 2023 inda yace yanzu Borno ta zama jiha mai lumana da kwanciyar hankali.

Wannnan na zuwa ne bayan tsohon shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai da manyan ‘yan siyasar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, suka bayyana goyon bayansu kan tazarcen Gwamnan inda suka kwatanta shi da Gwamnan da yafi kowanne aiki a tarihin jihar.

Yayin jawabi wurin ralin kaddamar da kamfen dinsa a filin wasa na Ramat dake Maiduguri a ranar Litinin cikin dandalin jama’a da suka hada da magoya bayansa da masu ruwa da tsarin APC, Zulum ya jaddada cewa a yanzu Borno lafiya kalau take kuma kwanakin farmakin Boko Haram sun shude a karkashin mulkinsa.

Ya ce a karon farko a tarihi, babu rahoton hari ko garkuwa da mutane na Boko Haram a kowacce karamar hukumar a jihar.

Yayi alkawarin tabbatar da karin karfin jami’an CJTF, mafarauta da ‘yan sa kai domin karfafa tsaro a Borno.

Zulum yayi kira ga masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar da su cigaba da goyon bayan gwamnatinsa da addu’o’i domin cika alkawurran kamfen dinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: