Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta mayar da martani kan zargin tsige shugaban karamar hukumar Ringim da ‘yan majalisar suka yi.

Shugaban kwamitin yada labarai Malam Muhammad Na’eem Adamu, ne ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani kan zargin tsige shi.
Ya ce ‘yan majalisar sun zarce kan iyakokinsu ne saboda ba su da irin wannan iko kamar yadda dokar kananan hukumomi ta 2012 ta yi wa kwaskwarima.

Ya yi bayanin cewa dokar kananan hukumomin Jihar Jigawa ta 2021 da aka yi wa kwaskwarima ta kara wa’adin kananan hukumomin zuwa shekaru uku tare da bai wa gwamnan jihar da majalisar dokokin jiha ikon tsige shugaba, mataimakin shugaban karamar hukuma ko kansila daga mukaminsa kan duk wani rashin da’a.

Malam Muhammad Na’eem, ya ce majalisun na da damar gabatar da zarge-zarge a kan shugaba ko mataimakinsa yayin da majalisar za ta kafa kwamiti da zai binciki lamarin domin ci gaba da daukar mataki.
Ya shawarci ‘yan majalisun da ke fadin jihar da su rika bin hanyoyin da suka dace da doka ta tanadar wajen gudanar da ayyukansu na majalisa.
Tun da farko majalisar dokokin karamar hukumar Ringim ta sanar da tsige shugaban karamar hukumar, Alhaji Shehu Sule Udi.
Takardar tsigewar ta samu sa hannun kansiloli takwas cikin goma na majalisar karamar hukumar da suka zargi shugaban karamar hukumar da laifin aikata rashin da’a.