Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa tana duba yiwuwar sanya haraji a harkokin sadarwar kasar wanda ta dakatar a baya.

Jaridar Punch ta rawaito cewa a yau Juma’a ta sake yin duba akan sanya haraji wanda za a aiwatar da shi a shekarar 2023 mai kamawa.
Hakan na zuwa ne ta cikin wata wasikar gayyata da kwamitin fannin tattalin arziki na Majalisar tarayya ya fitar domin yin nazari akan kudirin tattalin arziki shekarar 2022 da muke ciki wanda za a tattauna a zauren majalisar wakilai.

Kwamitin ya bayyana cewa zai zauna da mutane domin jin ra’ayoyin su akan kudurin tattalin arziki shekarar da muke ciki tare da yin duba a fannin haraji.

Sanarwar ta ce Najeriya za ta ringa karbar haraji daga kamfanonin sadarwa karkashin sashi na 13 na wannan doka.
A cikin sanarwa da kwamitin ya fitar bai bayyana adadin harajin da za a dinga yankewa kamfanonin ba.