Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar na fuskantar karancin ma’aikata akalla 3000.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Muhammad Makusidi ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis ga manema labarai bayan kammala kasafin ma’aikatar sa na shekarar 2023 mai zuwa a Majalisar dokokin Jihar.

Makusidi ya ce da yawa daga cikin jami’an Lafiyan na Jihar suna kasashen ketare inda su ka tafi sakamakon matsalar tsaro da ta addabi Jihar wanda Asibitoci ma ba su tsira ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa hakan ne ya sanya gwamnatin Jihar take biyan sauran likitocin da su ka rage a Jihar hakkokin su yadda ya kamata.

Dokta Muhammad ya kara da cewa Jihar ta samu asarar matasan ma’aikata a fannin lafiya wanda su ka tafi kasashen ketare domin yin aiki acan.

Mukusidi ya ce a baya ana samu likitoci 15 zuwa 20 wanda yanzu akan samu bakwai wanda hakan ya kawo karancin su sosai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: