Gwanatin tarayyar Najeriya ta zargi ɗan takarar shugaban ƙasa a jam”iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar kan shirin ta’azzara matsalar tsaro da rashin aikin yi a ƙasar.

Minsitan yaɗa labarai da raya al’adu a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da haka ind ayake sukar furucin ɗan takarar wanda ya yi a jihar Katsina.

Ya ce jam’iyyar PDP na shirin mayar da Najeriya baya daga cigaban da gwamnatin shugaba Buhari ta samar.

A furucin da ya ce ɗan takarar ya yi a jihar Katsina har da shigo da isashshen abinci wanda hakan na iya raba miliyoyin manoma da aikin su.

Lai Mohammed ya ce Atiku ya furta a Katsina cewar zai wadata ƙasar da makamai wanda hakan na iya ta’azzara matsalar tsaro.

Sai dai minsitan ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta yi namijin ƙoƙari wajen ganin an samar da kamfanonin shinkafa wabnda hakan ya sa ta zama a gaba-gaba cikin ƙasashen da ke samar da ita.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: