Wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilai a Najeriya sun kuduri aniyyar tilastawa babban bankin kasa CBN na dakatar da aniyar sa da ya sanya na kayyade adadin kudaden da za a dinga cirewa a kowacce rana.

A dokar da babban bankin ya sanya a mako gudu mutum zai cire naira 100,000 yayin da kamfani kuma zai cire naira dubu 500,000 daga bisani kuma bankin ya mayar mutane suma za su iya cire naira dubu 500,000 a mako.
Daya daga cikin shugabanni a majalisar ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa mafiya yawa daga cikin su sun yarje da a dakatar da dokar bakin daya.

Tun da fari majalisar ta nemi da bankin na CBN da ya dakatar da dokar wadda ya ce zata fara aiki a ranar 9 ga watan Janairun 2023 mai kamawa harsai gwamnan bankin godwin Emefele ya bayyana agaban majalisar.

Bayan aike masa da takardar gayyata da majalisar ta yi Emefele bai amsa gayyatar ba inda ya sanar da cewa ya tafi kasar wasu domin bincikar lafiyarsa.