Jami’an rundunar ‘yan sanda a Jihar Filato sun samu nasarar kama wani dan bindiga wanda yake karbar kudaden fansa bayan ya sace mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bartholomew Onyeka ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a a a yayin holan masu laifi a hedkwatar hukumar da ke garin Jos.

Kwamishinan ya ce an kama masu laifin ne a ranar 21 ga watan Disamban da muke ciki bayan samun bayanan sirri da su ka yi.

Ya ce wanda aka kama mai suna Ashiru Ibrahim mai shekaru 22 wanda ya kasance mazaunin Angwan Rogo yayi garkuwa ne da wani yaro mai shekaru hudu mai suna Abubakar Nazifi mazaunin zam-zam da ke Abuja Mata Rikkos a garin na Jos a ranar 19 ga watan Disamba.

Onyeka ya ce bayan kama wanda ake zargin ya sanarwa da jami’an ya boye yaron ne a maboyar su da ke Jihar.

Kazalika onyeka ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kira mahaifin yaron domin ya bashi kudin fansa naira miliyan uku.

Kwamishinan ya kara da cewa bayan kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukuncin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: