Gobara ta kone wani katafaren gini a karamar hukumar Hadejia da ke Jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi, inda gobarar ta lalata shaguna da dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), a jihar, CSC Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da karfe 3:00 na dare a Nane Plaza da ke kan titin Kano zuwa Hadejia.

Ya yi bayanin cewa shaguna 28, motoci biyu, da babura biyu da aka ajiye a cikin harabar wurin da lamarin ya shafa ne suka kone.

Adamu ya ce ba a yi asarar rai ba, amma gobarar ta cinye dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: