Kungiyar As’habul Kahfu Warraqeen reshen jihar Bauchi ta sha alwashin daukaka kara dangane da hukuncin kisa da wata kotun shari’a ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a kwanakin baya.

A wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a ranar Litinin ta yi watsi da hukuncin da alkali Ibrahim Sarki Yola ya yanke tare da misalta hukuncin a matsayin wanda ke cike da kura-kurai da kuma son zuciya a ciki.
Da ya ke karanta matsayarsu ga ‘yan jarida a shalkwatar ‘yan jarida da ke Bauchi (NUJ), Abdullahi Musa, Kakakin kungiyar, ya ce, da gangan Alkalin ya sauya batutuwan da suke akwai domin kaiwa ga matakin yanke hukuncin kisa ga malamin nasu.

Kungiyar ta zargi gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kitsa komai domin cimma manufarsa na dakile aniyar Abduljabbar Kabara bisa sukarsa da yake yi kan rashawa da cin hanci.

Musa ya ce, sun cimma matsayar daukaka kara ne zuwa kotun sama domin neman hakki ta hanyar shari’a, domin kwata-kwata ba su amince da hukuncin Ibrahim Sarki Yola ba, kuma abubuwan da aka yi wa malaminsu ya saba wa dokokin kare hakkin jama’a musamman dokar ‘yancin yin addini yadda mutum ya fahimta kamar yadda ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Kungiyar ta jero wasu da ta zarga da cewa su ma sun taba yin batanci da suka hada da Qaribu Kabara, Abdulrazak Yahya Haifan, Abbas Jega, Jalo Jalingo, Ahmad Gumi, Abdulwahab Abdullah da Sani Rijiyar Lemo amma babu wani da ya tuhumesu, Saboda su na kusa ko tare da masu mulki, su na nan a cikin ‘yancinsu a yayin da su kuma shugabansu wanda babu laifin da ya yi yana kan fuskantar shari’a.
A cewarsu, zargin batanci da ake yi wa Abduljabbar Nasiru Kabara babu komai a ciki illa salon yakarsa da kokarin kawo karshensa hadi da bata masa suna ta kowace hanya da wasu wadanda ba su jin dadin wa’azinsa ciki har da gwamna Ganduje.