Ana zargin masu garkuwa da mutane da hallaka wasu mutane uku wanda ‘yan gida daya ne da kuma wani ‘dan acaba bayan sun karbi kudi.

Daily Trust ta ce ‘yan bindigan sun kashe wadannan mutane uku da mai acaban ne duk da an biya su har Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansarsu.

Wannan lamari ya auku ne a kusa da dajin Garin Dogo da ke karamar hukumar Lau a jihar Taraba a ranar Lahadin nan da ta wuce, 25 ga Disamban 2022.

Rahoton ya nuna mutanen da aka dauke a dajin Garin Dogo duk ‘ya ‘yan mutum guda ne, ‘yan bindigan sun ce dole sai an biya N100m kafin su sake su.

Wani dillalin shanu, Alhaji Musa shi ne mahaifin yaran, shi ne ya rika tattaunawa da ‘yan bindigan domin ganin ya iya biyan kudin da suka bukata.

Da samun N100m ya gagra, sai ‘yan bindigan suka yarda cewa a biya N60m domin a saki ‘ya ‘yan na Alhaji Musa da ‘dan acaban da ya je biyan kudin.

Bayan ‘yan bindigan sun karbe kudin da aka kawo, sai suka kashe duka mutane hudun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: