Manajan Daraktan Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya, Thimothy Zalanga, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bude wa ayarin motocinsa wuta, suka kashe dan sanda da ke tsaron lafiyarsa.

Zalanga ya ce shi da sauran mutane da ke motarsa sun tsallake rijiya da baya ne bayan ’yan bindigar sun bude musu wuta dab da shigarsu garin Kaduna, bayan dawowarsu daga Abuja.


Ya ce an harbe Sufeto Aminu Muhammad da ke zaune a kujerar gaba har lahira, shi da direban da Sajan Allen Moses kuma sun tsallake rijiya da baya.
Ya ci gaba da cewa, abin ya faru ne a lokacin da Sufeto Aminu yake tsaka da waya da iyalansa cewa ya kusa zuwa gida.
A ziyarar ta’aziyyarsa ga Ofishin ’Yan Sanda na unguwar Donwn Quarters da ke Kaduna, Zalanga ya ce ’yan bindigar sun kai musu harin ne da misalin karfe 9 na dare ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, 2022.
Ya yi addu’ar samun rahama ga Sufeto Aminu Muhammad, tare da alkawarin cewa kamfanin zai ci gaba da tallafa wa iayalansa.
Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya wani rukuni ne karkashin Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya.