Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati a ƙasar domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Villa.
Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasar ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata a ƙasar, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa.

Da aka tambaye shi sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, ministan ya tabbatar da hakan, inda ya ce kwamitin albashi da shugaban ƙasar ya kafa na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumar albashin ma’aikata na ƙasar nan.

Kan batun albashin wata takwas da malaman jami’o’in ƙasar ke buƙatar gwamnati ta biya su kuwa, Ministan ya ce batun na gaban kotu.