Connect with us

Labaran jiha

Gwamnatin Zamfara Za Ta Dauki Mutane 2,000 Da Za Su Yi Aikin Yakar Batagari

Published

on

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umarnin daukar ma’aikata 2,000 wadanda za su yi aikin yakar ta’adar shaye-shaye da daba a Jihar.

Shugaba a kwamitin yaki da daba da shaye-shaye a na Jihar Bello Bakyasuwa ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin Jihar a ranar Alhamis.

Bakyasuwa ya ce gwamnatin ta bayar da umarnin daukar ma’aikata wanda su ka hada da maza da mata domin su yi aikin tabbatar da tsaron al’umma ba tare da nuna bangaranci ko siyasa ba.

Shugaban ya kara da cewa a halin yanzu mutane 6,000 ne su ke neman amma mutane 2,000 kawai za a iy dauka.

Bakyasuwa ya ce matakin daukar ma’aikatan da gwamnatin ta yi na daga cikin shirin ta fadada yaki da ayyukan daba da shaye-shaye a tsakanin matasa a dukkan fadin Jihar.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa baya ga aikin yakar daba da shaye-shaye, ma’aikatan za kuma su yi aikin yakar sauran laifuka daban-daban a Jihar.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Gwamnan Legas Ya Yiwa Fursunoni Afuwa

Published

on

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayar da umarni sakin fursunoni 55 daga gidajen gyaran hali daban-daban na fadin jihar.

Kwamishinam shari’a na jihar, Lawal Pedro, SAN, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu.

Gwamna ya amince da sakin mazauna gidan gyaran halin ne bisa shawarwarin da majalisar duba yiwuwar yiwa fursunoni afuwa ta jihar.

Continue Reading

Labaran jiha

Babu Batun Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Abba – Gwamnatin Kano

Published

on

Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.

Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.

Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.

Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.

Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.

Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.

Continue Reading

Labaran jiha

Gwamnatin Kwara Za Ta Bai’wa Ma’aikatan Jihar Tallafi

Published

on

Gwamnan Jihar Kwara Abdurrahman Abdulrazak ya amincewa da bai’wa ma’aikatan Jihar, Alawus-alawus da ake bai’wa ma’aikata kowanne wata.

Kwamishiniyar kudi ta Jihar Hauwa Nuru ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X na gwamnatin Jihar a yau Litinin.

Kwamishinar ta ce daga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin a Jihar, ciki harda ma’aikatan Kananan hukumomin Jihar.

Nuru ta ce shirin bai’wa ma’aikata tallafin kudin zai gudana na ne tsawon watanni uku daga watan Oktoba da ya gabata zuwa Disamba mai kamawa.

Nuru ta bayyana cewa bayar da tallafin zai taimaka matuka wajen rage tasirin sauyin da aka samu a harajin PAYE, wanda ake cirewa bayan samar da sabon mafi karancin albashin ma’aikatan.

Acewar Hauwa tallafin na a matsayin abin da ya dace domin tallafawa ma’aikatan, a lokacin da suke kokarin sabawa da sabon tsarin PAYE da aka samar bisa dokar harajin shiga na sirri.

A karshe Kwamishinar ta bukaci ma’aikatan Jihar da su tabbatar da ganin sun yi rajista da hukumar rajista ta jihar KWSRRA, inda ta bayyana cewa dukkan wanda bashi da rajistar ba zai samu alawus din ba.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: