Rindunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu gungun mutanen goma wanda ake zargin su da kai hare-hare birnin tarayya Abuja da Jihar Nasarawa.

Kwamishinan ‘yan sandan birnin na Abuja Abubakar Sadiq a lokacin da ya ke gabatar da su a gaban manema labarai.

Abubakar Sadiq ya ce wandanda ake zargi an kama su ne a wani Otal da ke yankin masaka zuwa Abuja.

Kwamishinan ya bayyana cewa a yayin kamen an kama su da bindiga kirar AK47 guda Biyar da kananan bindigogi guda uku da kuma kwanson harsasai 22.

Sauran kayan sun hada mota kirar Toyota Camry 2000 da injina gida biyu sai katin aikin wani dan sanda.

A yayin holan rundunar ta kuma kama wasu ‘yan ta’addan hudu da su ke yin fashi da makami a unguwar maitama da ke Birnin na Abuja tare da yiwa wani mutum mai sana’ar POS fashin kudade.

Sadik ya ce suma a hannun su an samu kananan bindugu guda uku harsasai 14 talabiji biyu wayoyin hannu da sauran wasu kayayyakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: