Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi wa fursunoni 39 da aka yankewa hukunci kan laifuffuka daban-daban a gidan gyara hali na Gusau, babban birnin jihar.

Da yake aiwatar da sakin fursunonin, Matawalle ya ce wannan na daga cikin shirin jin kai na gwamnatinsa a fadin sassan jihar.

Matawalle wanda ya samu wakilcin Atoni Janar na jihar, Alhaji Junaidu Aminu, ya bayyana cewa an fara shirin afuwan ne tun a watan Maris din shekarar nan inda wani kwamiti da Atoni Janar din ke jagoranta ya tantance fursunonin.

Gwamnan ya yi bayanin cewa fursunonin da suka koyi kyawawan halayya kawai sune suka ci gajiyar wannan shiri.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rahoto cewa kwamitin ya zabi fursunoni 46 da aka yanke wa hukunci daban-daban, ciki harda masu daurin watanni shida da daurin shekaru 20.

Hakazalika akwai wasu fursunoni 11 da aka yankewa daurin rai da rai sannan wasu biyar da aka yankewa hukuncin kisa.

Daga cikin fursunonin da aka tantance, an saki 30 da aka yankewar daurin watanni shida zuwa shekaru 20 da wasu tara da aka yankewa daurin rai da rai. An kuma rage hukuncin kisa da aka yankewa wasu biyar zuwa daurin shekaru bakwai a gidan yari.

Gwamnan ya yi kira ga wadanda aka yiwa afuwan da su kasance jakadu nagari a cikin al’ummarsu tare da yi musu gargadin kada su sake aikata wani laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: