Nijeriya ta kulla yarjejeniya da kasar Masar don inganta noman shinkafa ‘yar cikin gida.

Kasar dai ta kasance tana fama da matsanancin karanci da tsadar kayan abinci kama daga hatsi zuwa kayan masarufi, musamman shinkafa wadda aka fi amfani da ita a kowane lokaci.

A yanzu haka dai, kungiya manoman shinkafa  ta kasa da wani kamfani mai zaman kansa a Nijeriya sun  sa-hannun ne don a kara wadata kasar nan da shinkafa.

Hakazalika, a cikin watan Okotobar shekarar 2022, matsin tattalin arzikin Nijeriya ya karu da kashi 21.09 a cikin dari, inda wanannan alkalumman sun kasance mafi munin halin matsin tattalin arzikin da kasar ta taɓa shiga a tarihi.

Bisa ga wani  bayani na sakamakon binciken hukumar kididdigar farashin kayan masarufi ta bayyana cewa, ta auna kimar canjin kudi a kan farashin kaya da ayyuka, inda ta gano sun yi gudun wuce sa’a har i zuwa karin kaso 21.09 sabanin yadda yake a kaso 20.77 a watan Satumban bana.

A wata sabuwa kuwa, kasashen turai, zai fara zawarcin son kara karfafa alakar ciniki ta da kasar nan.

A cikin wannan shirin dai,  kasashen na turai, za su fara yi a wajen iyakokinta.

Ta sanar da cewa, za ta fara shirin ne ganin yadda wasu kasahsne da ke a Afirka kamar Nijeriya Kamaru da Kongo da Tanzania da Zimbabwe ke fustantar kalubale a fannonin nomansu.

Bugu da kari, ana sa ran zai bi sahun sauran kasashen Afirka guda 7 da aka fara gudanar da shi a baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: