Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa Kanal Lawan Rabi’u ‘Yandoto mai ritaya a lokacin da ya ke tsaka da tafiya zuwa garin ‘Yandoto da ke karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe shida na yammacin ranar Lahadi a yayin kwanton baunar da su ka yiwa tawagar Kanal din.
Wata majiya daga Jihar ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa ga Kanal Lawan ne tare da ‘ya’yansa biyu da wasu mutane.

Majiyar ta kara da cewa Kanal din yana dab da shiga garinnasu maharan su ka fara harbe-harbe wanda hakan ya tilastawa mazauna kusa da yankin tserewa.

Majiyar ta ci gaba da cewa an gano ‘yan bindigan ne sun yi garkuwa da Kanal Lawan ne bayan da al’ummar kusa da gurin su ka samu motar sa babu kowa a ciki.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar bai ce komai ba danga ne da faruwal lamarin.