Hukumar zabe ta kasa iNEC ta sake fitar da sanarwar jan hankali da gargadin al’umma kan kiyaye kansu daga shiga shafukan neman aiki a yanar gizo da nufin samun aiki wucin gadi a hukumar na babban zaben shekarar 2023.

Sanarwar hakan ta fito ne daga babban mai

magana da yawun shugaban hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, a yau Talata a Abuja.

Oyekanmi ya ce shafin da ake yada wa na karya ne, kuma ana yaudarar mutane ne tare da zaluntar su. Inda ya ce zuwa yanzu hukumar ba ta fitar da wani tsari na dibar

ma’aikata domin yin aikin zabe na wucin gadi ba.

Ya cigaba da cewa shafin hukumar ta INEC wanda ake neman aiki da tantancewa yanzu haka a rufe yake.

Irin wannan kira dai hukumar ta sha yin sa don jan hankalin mutane akan su gujewa shiga hannun bata gari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: