Labaran jiha
NDLEA Ta Kama Mutane 977 Da Su Ke Safarar Kwayoyi
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wasu mutane 977 da take zargi da ta’ammuli da safarar miyagun kwayoyi a jihohin Adamawa da Taraba da Gombe a shekarar 2022.
Hukumar ta kama jimillar kilo 2,757 na tabar wiwi da sauran magungunan asibitin masu tabin hankali cikin shekarar da ta gabata.
Idris Mohammed Bello, kwamandan shiyyar da ke kula da jihohin Uku na Adamawa da Taraba da Gombe ne ya fitar da wannan kididdigar a ranar Talata a hedikwatar shiyyar da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Bello, ya kara da cewa, daga cikin mutane 977 da aka kama, an yanke wa 365 hukunci, yayin da 374 ke karbar nasihohin gyaran hali.
Rahoton hukumar na shiyyar a shekarar 2022 ya nuna cewa, Hukumar ta kama kilo 1,808 na tabar wiwi da kuma kilo 949 na magungunan asibitin masu tabin hankali (kilo 2,757 ) daga wadanda ake zargin a jihohin uku a shekarar da ta gabata.
A cewarsa, mafi yawan mutanen 457 sun fito ne daga jihar Adamawa yayin da aka kama 290 daga Taraba sai 230 daga Gombe.
Hukumar ta NDLEA ta kama kimanin kilo 1,241.56 na tabar wiwi da muggan kwayoyi a cikin jihar Adamawa a shekarar 2022, yayin da aka kama kilo a Taraba 882.149 da kilogiram 635.993 a Gombe.
Labaran jiha
Gwamnatin Jihar Kano Ta Soke Komawa Makaranta Ranar Litinin
Gwamnatin jihar Kano ta soke komawar ɗalibai makaranta ranar Litinin.
Hakan na kunshe a wani sakon murya da kwamishinan ilimi a jihar Umar Haruna Doguwa ya sanar.
Ya ce an dakatar da komawa makarantar ne saboda wasu abubuwa dasu ka taso.
Sannan ya ce za a sanar da ranar komawa nan gaba kaɗan.
Kwamishinan ya bai wa iyaye hakuri dangane da jinkirin da aka samu.
Labaran jiha
Ambaliyar Ruwa – Mutane 20 Sun Mutu A Yobe
Mutane 20 ake fargabar sun mutu yayin da mutane 3,000 su ka rasa muhallinsu a jihar Yobe.
Shugaban ƙaramar hukumar Bade Babagana Ibrahim ne ya bayyana haka ya ce lamarin ya faru sakamakon ruwan kamar da bakin ƙwarya.
Ya ce gwamnatin na ƙoƙarin samar da kayayyakin agaj kamar abinci, magunguna, da taftataccen ruwan sha don kare su daga kamuwa daga cutuka.
Sai dai ya ce akwai buƙatar agajin gwamnatin tarayya duba ga yawan masu gudun hijirar.
Shugaban ya ce makonni biyu kenan aka shafe ana samun ruwan sama wanda ya yi sanadiyyar ambaliya.
Lamarin ya shafi Gashua tare da umartar mutanen da ke rayuwa a wuraren da ambaliyar na iya shafa da su kauce tare da barin gidajensu.
Labaran jiha
Bayan Ɓarkewar Zanga-zangar Kan Tsadar Man Fetur Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Umarnin Fito Da Manyan Motoci Da Ɗaukar Mutane Kyauta
Gwamnan jihar Kwara Abdurrahman Abdurrazak ya bayar da umarnin fitar da motoci a kwaryar birnin jihar don saukaka harkar sufuri.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan da jama’a ke kokawa danane da tashin farashin man fetur a ƙasar.
Babban sakataren yaɗa labaransa Rafiu Ajakaye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce za a ɗauki mutane zuwa manyan wurare kyauta
Wannan dai na zuwa ne yayin da masu ababen hawa su ka tafi yajin aiki sanadin ƙarin farashin mai wanda hakan y sa fasinjoji su ka yi cirko cirko a tituna.
Gwamnan ya bai wa jama’ar jihar hakuri dangane da halin da ake ciki na tsadar man fetur.
-
Labarai7 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari