Wasu dakarun Sojin Sama sun rasu, wani daya ya samu mummunan rauni sakamakon kwacewar da wata tirela ta yi ta bi ta kansu a Jihar Kwara.

 

Lamarin da ya faru a daidai gadar Pasa a yankin Eyenkorin daf da Barikin Sojin Sama, ya haifar da rudani a tsakanin sojoji da mazauna yankin.

 

Sakataren Kwatin Zartarwa na Jihar Kwara, Shola Musa, ya ce lamarin ya faru sakamakon tsinkewar birkin tirelar.

 

“Na kira rundunar ’yan sanda su je wajen da lamarin ya faru don tabbatar da doka da oda sakamakon rudani da aka shiga a yankin,” kamar yadda ya bayyana wa Daily Trust.

 

A lokacin da wakilanmu ya ziyarci yankin a ranar Talata, ya iske motar sojin sama mai lamba AF 496 CO1 girke a wajen da lamarin ya faru tana jiran ko ta kwana.

 

A cewar wani ganau, da ya ce sunansa Alhaji Pasa, “Dakarun suna cikin aiki lokacin da burkin tirelar ya tsinke ya murkushe biyu daga cikinsu ta ji wa daya mummanan rauni a shingen bincikensu.

 

Kakakin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) na Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya ce, “Na samu labari, amma ba ni da cikakken bayani game da abin da ya faru, watakila an kwashe wadanda abun ya rutsa da su kafin mutanenmu su je wajen.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: