Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin yin adalci ga kowa, idan aka zabe shi.

Tinubu ya yi wannan alkawarin ne a wani taro da ya yi da shugabannin Musulmin Arewa maso Yamma a Kano.
Tinubu ya yi alkawarin yin adalci da bin ka’idojin Addinin Musulunci.

Ya ce shugaba a jam’in sallah an umarce shi ya zama shugaban kowa, Idan aka zabe shi, zai yi mulki bisa gaskiya da dimokuradiyya, bisa tsarin mulkin kasar Najeriya.

Zan yi kokari ya zama mai aminci kuma mai kwazo.
Ya kara da cewa zai yi kokarin inganta rayuwar dukkan mutanensu, Kirista ko Musulmi.
Tinubu ya ce manufarsa, ita ce hadin kai, ci gaba da kuma daidaito don ci gaban
Nijeriya.
Ya yi alkawarin farfado da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa da rashin tsaro ta hanyar samar da kayan aiki na zamani ga hukumomin tsaro.