Akalla manoman shinkafa 20 ake fargabar sun rasu sakamakon kifewar jirgin ruwa da dare a yankin Karamar Hukumar Koko/Besse da ke Jihar Kebbi.

Shugaban Karamar Hukumar Koko/Besse, Yahaya Bello, ya ce iftila’in ya auku ne a lokacin da jirgin ruwan ke dauke da manoma kimanin 100 a ranar Talata.

Fasinjojom da lamarin ya shafa kusan baki dayansu matasa ne, maza da mata, sun gano gawarwakin mutum 10, hudu mata da maza shida.

Ya ce sun ceto kimanin mutum 80 kuma suna ci gaba da bincike domin gano sauran da suka bace.

Ya ce hatsarin ya auku ne a lokacin da manoman shinkafan ke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Samanaji.

Shi ma dai kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar iftila’in.

Leave a Reply

%d bloggers like this: