Hukumar kula da farashin man fetur ta Najeriya ta garkame a kalla gidajen 14 , NMDPRA reshen jihar Kano ta dauki matakin ne saboda yadda suke siyarwa kwastomomi kayayyakinsu sama da farashin da aka ka’idance.

Hukumar kula da farashin man fetur da jihar Kanon ta garkame gidajen mai masu zaman kansu ne, saboda yadda suke sai da man fetur kan N290, N295 da N300 duk lita daya.


Yayin zantawa da manema labarai game da hukuncin, shugaban NMDPRA na Kano, Aliyu Muhammad Sama ya ce, duk da ba a saran ‘yan kasuwa su saida mai kan farashi mai sauki kamar na manyan ‘yan kasuwa, amma bai kamata su sanya farashi dai tsauri haka ba.
TheCable ta rahoto, a cewarsu gidajen mayukan sun janyo hukuncin kwace lasisinsu ko kuma cinsu tarar N150,000 ga duk wajen bada mai daya.
Idan ka duba, gidajen man gwamnati na saidawa kan farashi mai sauki na N185 duk lita daya.
An san ba abu bane mai yuwuwa a ce ‘yan kasuwa su siyar kan wannan farashin, duba da yadda suke ikirarin suna siya kan farashi mai tsada.
Haka zalika, shugaban hukumar ta jihar ya kara da cewa, hukumar daidaita farashin ta dakatar da kasuwancin ‘yan kasuwa 16 don ta horar dasu kan abun da suka aikata.