Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta jinjinawa al’ummar Najeriya dangane da yadda su ke fito domin karbar katunan zaban su a ofisoshin hukumar.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a Festus Okoye ne ya bayyana hakan a yayin ganawar sa da gidan talabijin Channels.


Kwamishinan ya danganta fitowar al’ummar da yadda shugabanni a matakai daban-daban ke ci gaba da wayar da kan al’umma kan fito karbar katunan zaben su.
Kazalika Okoye ya ce hukumar ta fuskantar matsaloli akan yadda wasu ba sa sanin hanyar da za su bi domin karbar katunan zaben su.
Festus Okoye ya kara da cewa ba za su buga katunan zaben mutanen da su ka yi ya haura daya domin har kawo yanzu katunan su yana ci gaba da aiki.
Sannan ya ce dukkan wadanda su ka sauya guraren gudanar da zabe za su iya karbar katunan su a guraren da ake karba.