Hukumar sufurin Jiragen kasa ta NRC ta Jihar Ondo ta bayyana dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa da ke Jihar Edo.

Dakatarwar na zuwa ne a ranar Lahadi sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai tashar jiragen tare da yin garkuwa da fasinjoji.

Jaridar Puch ta rawaito cewa hukumar ta sanar da cewa matakin da ta dauka ya zama wajibi bayan matsalar tsaro da ta addabi Jihar.

NRC ta ce ba za ta bude tashir ba sai lokacin da hukumar ta sanar.

‘Yan bindigan sun kai harin ne dai a ranar Asabar inda su ka yi awon gaba da tarin fasinjoji masu yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: