Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da yawa daga tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo a karshen makon nan.

Rahoton Daily Trust ya nuna wadannan Bayin Allah da aka dauke su na shirin shiga jirgin kasan da zai je birnin Warri ne a lokacin da aka kawo harin.


Majiyoyi da-dama sun tabbatar da aukuwar wannan labari mara dadi a yammacin Asabar.
Jaridar ta ce babu tabbacin ko wasu sun rasu sa a sanadiyyar harin, amma shakka babu akwai wadanda suka samu rauni a dalilin harbin bindigogi.
Jami’in hulda da jama’a wanda yake magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan reshen jihar Edo, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Nwabuzor ya ce wadannan miyagu sun aukowa tashar jirgin ne dauke da bindigogin AK-47 a ranar Asabar da yamma, sai suka rika harbe-harbe ko ta ina.
Bayan sun razana jama’a, jami’in ‘dan sandan ya ce ‘yan bindigan suka yi awon-gaba da matafiya. Jawabin jami’an tsaron ya nuna cewa an baza dakaru domin gaggawar ceto wadanda aka dauke daga hannun wadannan masu garkuwa da mutane.
Punch ta ce harin yana zuwa ne watanni bayan an tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a wani kauye mai suna Katari, inda aka yi garkuwa da fasinjoji.
Rahoton da aka fitar cikin daren Lahadin nan ya tabbatar da cewa harin ya raunata mutane da yawa. Sai dai babu adadin wadanda ta’adin ya rutsa da su.