Gwamnatin jihar Edo, ranar Lahadi, ta sanar da cewa an kama wani mutum daya da ake zargin yana da hannu a sace Fasinjojin Jirgin kasa a tashar Igueben ranar Asabar.

An kawo rahoton cewa akalla Fasinja 30 yan bindiga suka sace wadanda ke jiran Jirgin kasa a tashar dake karamar hukumar Igueben da misalin karfe 4:00 na yamma.

Da yake jawabi ga manema labarai kan lamarin, kwamishinan sadarwa da wayar da kai na Edo, Chris Osa Nehikhre, ya bayyana harin da abu mai walaha da gwamnati ta taba gamuwa da shi.

Nehikhre ya kara da cewa nan take bayan faruwar lamarin yan sanda da sauran jami’an tsaro suka bazama dazuka da nufin ceto Fasinjojin da kama maharan.
A cewarsa Kokarin da ake ya fara haifar da sakamako mai kyau domin an kama mutum daya ada ake zargin dan tawagar masu garkuwan ne kuma ya fara bayani.