Gwamnatin Jihar Anambra ta bayyana cewa za ta fara gudanar da bincike akan mutumin da ya hallaka matar sa akan ta cinye biredin ‘ya’yansu.

Kwamishiniyar mata da walwala ta Jihar Misis Lfy Obinabo ta tabbatar da hakan a yayin wata ganawa da ta yi da mahaifiya ga matar da ta rasa ranta a ranar Laraba.
Kwamishinar ta ce ya zama waji gwamnatin Jihar da zurfafa bincike akan lamarin cikin gaggawa.

Lfy ta kuma yi kira ga mata da su tashi tsaye su yaki duk wani cin zarafi da su ke fuskanta a gidajen Auren.

A yayin jawabin mahaifiyar marigayiyar ta bayyana cewa bayan aika-aikar da mijin ‘yartata yayi ya tsere.
Cordella ta bukaci gwamnatin da ta zurfafa bincike domin kamo wanda ake zargi tare biwa ‘yartata hakkin ta.