Direbobin Manyan motoci da su ka rufe kan hanyar Zariya zuwa Kano sakamakon hallaka wani direban motar da wani jami’an soji yayi.

Direbobin sun bude hanyar ne a safiyar yau Asabar bayan sanya motocin su da su ka yi akan hanyar.

Direbobin sun dauki matakin hakan ne bayan wata tattaunawa da su ka yi da jami’an tsaro da jami’an hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa FRSC.

Mai rikon mukamin kwamandan hukumar FRSC na Jihar Kaduna Lawan Garba ne ya tabbatar da hakan a yau Asabar inda ya ce kawo yanzu komai ya daidaita akan hanyar.

Lawal ya ce an bude hanyar ne da misalin karfe 9:30 na safiya bayan shafe kwanaki uku a kulle.

Lawal Garba ya kara da cewa kawo yanzu ababen hawa na ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: