Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ceto wasu mutum 30 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Nasarawa.

 

Lamarin na zuwa ne yayin da rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ ta fafata da ’yan bindigar a yankin Idu, Chikara da ke iyaka da Karamar Hukumar Toto ta Jihar Nasarawa da kuma Abaji da Koton Karfe a Jihar Kogi.

 

Mataimakin Daraktan rundunar sojin, Kyaftin Godfrey Abaakpa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

 

Ya ce sojojin sun gudanar da kai farmakin ne tare da rundunar hadin gwiwa ta CJTF a Jihar Nassarawa.

 

Abakpa ya ce sojojin sun fatattaki ’yan bindigar tare da kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu da dama suka tsere.

 

Ya kara da cewa sojojin sun kuma kashe ’yan bindiga biyu.

 

A cewarsa, wani jami’in tsaro daya ya samu rauni a arangamar wanda kuma a yanzu yana asibiti yana jinya.

 

Rundunar ’yan sandan Najeriya da ke Karamar Hukumar Toto ta bayyana sunayen mutanen da aka ceto yayin da gwamnatin jihar ta taimaka musu wajen mika su ga iyalansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: