Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samu zarafin binciko sunayen likitocin bogi guda 199 wadanda gwamnatin ta ke biyan su albashi a Jihar.

Matawalle ya bayyana hakan ne a wajen taron manema labarai a gidansa da ke karamar hukumar Maradun ta Jihar.
Gwamnan ya ce ganowar na zuwa ne bayan tsaikon biyan albashi ma’aikatan lafiya da aka samu a Jihar.

Matawalle ya kara da cewa tsaikon biyan albashin na zuwa ne bayan gano damfarar da likitocin bogin su ke yi,amma daga bisani sun biya ma’aikatan albashin su na watan Nuwamba da Disamba.

Kazalika Matawalle ya ce ana biyan likitoci 280 albashi a Jihar ta samu nasarar gano likitoci 81 ne ke aiki a Jihar yayin da sauran su ka kasance na bogi.
Gwamnan Matawalle ya bayyana cewa bayan gano likitocin ya samu zarafin ganawa da kungiyar kwadago ta kasa NLC domin binciko likitoci 199 da ake zargi tare da amsar albashi daga gwamnati ba tare da yin aiki ba.
Gwamnatin ta Zamfara ta gano likitocin ne sakamakon tantancewa da gwamnatin ke yi karkashin jagorancin ofishin shugaban ma’aikata na Jihar,bisa yunkurin gwamnatin ke yi na fara gudanar da tsarin biyan albashi mafi karanci na Naira 30,000.