Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya hori ’yan siyasa da su rika bai wa bangaren shari’a damar gudanar da ayyukan da Kundin Tsarin Mulkin kasar ya tanada, yana mai cewa idanun ‘yan siyasa sukan rufe da zarar sun samu mulki.

 

Jonathan ya yi wannan nasihar ce a lokacin rufe liyafar karramawa da kuma kaddamar da littafi da aka kwashe tsawon mako guda ana yi wa Babbar Alkalin Jihar Bayelsa, Mai shari’a Kate Abiri da ta yi ritaya.

 

A taron da aka yi a Yenagoa, babban birnin jihar, Jonathan ya jaddada rawar da mai shari’a Abiri ta taka lokacin da ta rantsar da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda a cewarsa hakan ya dakile rikicin tsarin mulki a jihar.

 

Ya shawarci ‘yan siyasa a kan kada su rufe idanu saboda karfin da suke da shi, yayin da ya bukaci jami’an shari’a da su yi kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana da jajircewa wajen tabbatar da doka da oda, wanda ya ce yana da matukar muhimmanci wajen wanzuwar adalci.

 

Ya ce yana shawartar ’yan siyasa cewa, a lokacin da suke ganiyar mulki, kada su yi kokarin yi wa bangaren shari’a zagon kasa, saboda bangare ne da ya cancanci a kiyaye tsare-tsare da al’adunsa.

 

Idan suka samu mulki a siyasance, sai su runtse idanunsu, Saboda haka ya kamata ’yan siyasa su sani cewa al’umma tana lura da abin da ke faruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: