Wata mota kirar Sharon dauke da man fetur a cikin jarkoki ta kama da wuta a kofar shiga gidan man fetur na NNPC da ke Club Road, Murtala Mohammed Way a Kano.

A cewar wasu wadanda abin ya faru a idonsu, motar ta kama da wuta ne a yayin da ta ke shirin barin gidan man misalin karfe 5 na yammacin ranar Talata.


Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon lamarin, saidai direban motar ya samu karamin rauni.
Jafar Mohammad Ahmad wanda aka fi sani da Sanjo Badawa, shine wanda ya yi magana da manema labarai .
Ya ce maganar gaskiya, akwai masu babura fiye da 300 a cikin gidan man, sun ki sayar musu da mai, iya Kawai wadannan yan bunburutun (black market) suke sayarwa.
Mota daya za ta siya man fetur kimanin na N50,000 ita kadai hakan kuma yana bata lokaci, sun kawo man misalin karfe 11 na safe amma sun fara sayarwa misalin karfe 5 na yamma.