Rahotanni daga Jihar Nasarawa sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar Firemaran gwamnati da ke Alwaza cikin karamar hukumar Doma ta Jihar.

Lamarin ya farune a safiyar yau Juma’a a lokacin da daliban ke zuwa cikin makarantar domin daukar darasi.
Rahotannin sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da daliban makarantar wanda ba a san adadin su ba.

Bayan yin garkuwa da daliban har kawo yanzu ba a san idan maharan su ka nufa da daliban ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Rahman Nansel ne ya tabbatar da faruwal lamarin.
DSP Rahman ya ce bayan yin garkuwa da yaran tawagar Jami’an tsaron ‘yan sanda Soji da sa-kai su na ci gaba da gudanar da sintiri domin gano inda maharan su ka nufa.